23 Oktoba 2025 - 11:39
Source: ABNA24
An Buɗe Taron Sufuri Na Yanki A Islamabad

An bude taron yini biyu na ministocin sufuri na yankin gabashin Asiya, wanda gwamnatin Pakistan ta dauki nauyin shiryawa a birnin Islamabad tare da halartar ministan kula da hanyoyi da raya birane na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Malama Farzaneh Sadiq, ministar hanyoyi da raya birane, ita ce ke jagorantar tawagar kasar Iran a wannan taron.

Buɗe taron ya samu halartar shugabannin tawagogi daga kasashe 12, inda aka fara shi da jawabin Sanata Muhammad Ishaq Dar, mataimakin firaministan kasar kuma ministan harkokin wajen Pakistan, da Abdul Aleem Khan, ministan sufuri na kasar.

Your Comment

You are replying to: .
captcha